Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya sulhunta Sanata Barau da Abba Bichi

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sasanta mataimakin Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Shugaban kwamitin kasafin Kuɗi na majalisar wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, bayan rikicin siyasar da ya shiga tsakanin magoya bayansu.

Wannan na cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Sanarwar ta bayyana cewar an gudanar da taron sasancin ne a Abuja da sanyin safiyar Laraba, inda shugabannin biyu suka tattauna bambance-bambancen da ke tsakaninsu tare da amincewa da buƙatar haɗa kai domin moriyar jam’iyyar APC.

Gwamna Abba Yusuf ya buƙaci Sanata Barau da Abubakar Bichi da magoya bayansu su ajiye duk wani saɓani, yana mai cewa haɗin kai da fahimtar juna na da muhimmanci wajen samun nasarar APC a zaɓen 2027.

Gwamnan ya kuma gargadi magoya bayan shugabannin biyu da su guji zagin juna, ko kalaman tunzura jama’a da duk wani abu da zai iya ƙara raba kan ’yan jam’iyyar.

FB IMG

A nasu ɓangaren, Sanata Barau Jibrin da Abubakar Kabir Bichi sun buƙaci magoya bayansu da su guji duk wani abu da zai sake rura rikicin cikin gida, tare da tabbatar da goyon bayansu da jajircewarsu ga jam’iyyar.

Sun kuma gode wa Gwamna Abba Yusuf bisa shiga tsakani da kuma ƙoƙarin da ya yi wajen kawo ƙarshen rashin fahimtar da ke tsakaninsu.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Rikicin Masarautar Kano: Gwamna Abba ya yi ganawar sirri da na hannun daman Sarkin Kano

‎ ‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci...

‎Dalilin da yasa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya ziyarci Sarki Aminu Ado Bayero

‎‎Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

‎INEC ta bayyana Jihohin dake kan gaba wajen yawan masu katin zaɓe

‎ ‎Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta...

‎Rundunar Sojin Sama ta fitar da sunayen mutanen da suka mutu a hatsarin jirginta

‎ ‎‎ ‎Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bayyana sunayen...