Wata Kungiya ta Musanta Zargin Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa a Kano Free Trade Zone

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wata Kungiya mai suna Kano Coalition For Awareness on Accountability, ta musanta zargin cewa hukumar da ke kula da harkokin fitar da kayayyaki ta kasa (NEPZA) a jihar Kano, ta yi sakacin da ya jawo asarar biliyoyin Naira na kudaden shiga.

Kungiyar, a cikin wata sanarwa da shugabanta Sadi Tanko Surajo ya fitar kuma ta aikewa manema labarai a Kano, sannan ta bayyana zargin a matsayin mara tushe da kuma yunkurin bata sunan ‘yan kasuwa a jihar.

Kwankwaso ya bayyana wadanda suka hana gwamnan Kano sakat tsawon Shekara Daya

“Babu wani abu mai kama da ana yin sakacin a Cibiyar ciniki ba tare da tsangwama ta Kano ba, na shafe shekaru 10 ina gudanar da sana’ata a can, kuma duk zarge-zargen da na karanta a na yi musu, babu wanda zai iya tabbatar da shi”.

Lokaci ya yi da za mu bayyana wa mutane gaskiya kan lamarin. Ina kara maimaita wa, babu wani abu da ake yi da ya saba wa doka a Kano Free trade zone”.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake irin wannan zargi ba, kuma har yanzu hukumomi ba su gano wani abu da ake yi wanda ya sabawa doka a Cibiyar ciniki ta Kano ba. ” Yace

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...