Rundunar haɗin gwiwa dake yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safararsu ta tattauna da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya, domin ƙarfafa matakan yaƙi da matsalar, tare da duba hanyoyin samun ƙarin tallafin ci gaba ga jihar.
Shugaban rundunar, Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, ne ya jagoranci tawagar zuwa Ofishin Jakadancin Amurka, inda suka gana da Daraktan Ofishin Harkokin Miyagun Ƙwayoyi na Ƙasa da Ƙasa da Bin Diddigin Aiwatar da Doka (INL), Mista Tolliver Derrick, tare da wasu jami’an ofishin jakadancin.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa, tattaunawarta su ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safararsu ba bisa ƙa’ida ba.
Sanarwar ta ce, ɓangarorin biyu sun kuma tattauna batutuwan tattara bayanan sirri domin gudanar da ayyukan jami’an tsaro, ƙarfafa ƙwarewar hukumomi, bayar da taimakon fasaha, rigakafin shaye-shaye a cikin al’umma da kuma shirye-shiryen musamman na kula da masu buƙatar gyaran hali bayan shaye-shaye.
Ta ƙara da cewa, an ba da muhimmanci na musamman ga shirye-shiryen tallafa wa masu rauni a cikin al’umma, musamman matasa.
Haka kuma, tattaunawar ta duba hanyoyin haɗa shirye-shiryen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran shirye-shiryen gwamnatin Amurka da ake aiwatarwa a Jihar Kano.
Da yake tsokaci kan batun, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya bayyana cewa, ba za a iya samun nasara a yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta hanyar amfani da jami’an tsaro kaɗai ba, sai an haɗa da rigakafi, gyaran hali da kuma sa hannun al’umma.
Ya ce, “Yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi yana buƙatar fiye da ɗaukar matakan tilasta bin doka kawai. Ana buƙatar hukumomi masu ƙarfi, sa hannun al’umma, ingantaccen tsarin gyaran hali, rigakafi mai ƙarfi da kuma haɗin gwiwa da ƙasashen duniya.”
Rimin Gado ya bayyana cewa, rundunar na da sha’awar amfani da sauran shirye-shiryen tallafin Amurka a Kano domin samar da tsaro mai ɗorewa da kare rayuwar al’umma ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa.
A cewar sanarwar, Ofishin Jakadancin Amurka, ta hannun ofishin INL, ya nuna sha’awar yin aiki tare da rundunar, tare da nazarin hanyoyin haɗa ayyukan yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran shirye-shiryen tallafin fasaha da ci gaba da Amurka ke bayarwa a yankin.
Read also: Zargin badakala: Ka fito ka fasa kwan, in ka ki mu fasa maka mugunya- Waiya ga Baffa Bichi
Read also: Majalisar ta amince da Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano
Read also: Kadan ya rage da na nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano – Kwankwaso

Sanarwar ta ce, tattaunawar ta kuma shafi fannoni kamar kyakkyawan shugabanci, tsaron jama’a da kuma ƙarfafa juriyar al’umma wajen fuskantar matsalolin tsaro da zamantakewa.
A ƙarshe, sun amince da muhimmancin kafa tsarin haɗin gwiwa mai tsari da kuma ci gaba da tattaunawa domin ƙarfafa yaƙi da miyagun ƙwayoyi da inganta ci gaban al’umma.