Daga Zubaida Abubakar Ahmad
Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PRP , Salihu Tanko Yakasai ya bayyana kudirorinsa na ganin Kano ta yi fice idan aka zabe shi babban zaben a shekara ta 2033.
A cewarsa, kudirorin nasa sun hada da yadda za a mayar da Kano ta zama cibiyar kasuwanci ba kawai a Najeriya ba, har da kasashen Afirka baki daya a cikin shekaru 10 har ta wuce Legas.
Katin zabe ne damar talaka ta karshe don zabar shugabanni nagari – Kawu Sumaila
Tanko Yakasai wanda ake yiwa lakabi da Dawisun Kano ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ya bar wasu aiyukan cigaba a bangarori bakwai, kamar; bunkasa Tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, Inganta ilimi, lafiya da muhalli, sai inganta ma’aikatun gwamnati wato yadda za a gyara harkokin mulki gaba daya a jihar da kuma uwa uba inganta tsaro domin samun kwanciyar hankali da lumana.
“Ba wai kawai mun shiga Siyasa ido rufe bane,Muna da manufar bari wani abu da za’a dade ana tunawa dani, kuma hakan bazata samu ba sai idan mun mai da hankali wajen samar da ayyukan raya kasa, da kula da bukatun talakawa domin inganta rayuwar su su zamo abun kwatance a Cikin al’ummar Nigeria ” Inji Salihu Tanko Yakasai
Wadannan hanyoyi ne da muke ganin za mu iya gyara al’amuran Kano da kyau da kuma mayar da jihar zuwa mafi bunkasar tattalin arziki da wadata da za su ciyar da bangarori daban-daban na tattalin arzikin jihar gaba, kamar yadda na ambata wasu muhimman kudirori guda bakwai da Zamu mai da hankali akansu a matsayin manufofinmu”.
“Shirinmu cikakke ne kuma burinmu shine, ta yaya za mu sanya Kano ta zama cibiyar inganta kasuwanci ba kawai a Najeriya ba, har ma a Afirka a cikin shekaru 10, ta zarce Legas. Shi ya sa muka kiran shirinmu “Vision”. 2033″.
Karbar katin zabe wajibi ne ga duk dan kasa nagari – Falakin Shinkafi
Tanko Yakasai, wanda yake da kwarin gwiwar lashe zaben ya bayyana cewa, “Abin farin ciki, muna wakiltar rukunin al’umma mai matukar muhimmanci a jihar Kano wato matasa kuma muna da tabbacin cewa su ke da kaso 70% na al’ummar kasar za su zabi wanda zai wakilce su, wanda ya san bukatunsu kuma yake cikisu .
Mun ji ra’ayoyin jama’a, kuma mun tabbata cewa mutane suna son ‘canji’ a jihar nan, sun gaji da halin da ake ciki, sun gaji da irin wadannan mutanen da suka shafe shekaru ashirin suna mulkarsu, kuma tabbas suna buƙatar canji”.
Salihu ya kuma yi alkawarin cewa idan ya zama gwamna, gwamnatin sa za ta zama gwamnatin matasa, wacce matasa zasu gudanar domin nuna cewa suma zasu iya jagorancin al’umma.
“Zai ba ku sha’awar sanin cewa shugaban sashin kowane bangare da na ambata a sama zai kasance wanda bai kai shekara 40 ba amma kwararre kuma mai matukar kishi wanda zai iya tsayawa ko ina a duniya kuma a girmama shi a matsayinsa na wanda yasan me yake.
Bugu da kari, dan takarar gwamnan na PRP ya yi kira ga matasa da su fito su karbi katin zabe na dindindin kuma su guji yin rijista sau biyu wanda zai hana su kada kuri’a a zabe mai zuwa.