Sanata mai wakiltar yankin Kano ta Kudu, Suleiman A. Kawu Sumaila, ya ce gagarumin tallafin kayan aikin gona da ya kaddamar da kashi na farko na rabon zai sauya fasalin noma tare da inganta rayuwar al’ummar yankin.
A jawabinsa yayin taron, Sanata Kawu ya bayyana wannan mataki a matsayin gagarumi da tarihi ba zai manta da shi ba. Ya ce shirin na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke gudanarwa a karkashin shirin Renewed Hope Agenda, wadda ya mayar da hankali wajen inganta samar da abinci da bunkasa tattalin arzikin al’ummar karkara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa sa hadimin Sanatan Kawu kan harkokin yada labarai Abbas Adam Abbas ya aikowa Kadaura24.

Sanatan ya yabawa yan majalisar tarayyar da suka fito daga Kano ta Kudu, musamman Hon. Kabiru Alhassan Rurum, da kuma shugabannin jam’iyyar APC na jihar. Ya bayyana cewa fiye da manoma da10,000 ne su ka amfana a zangon farko — wanda ya ce ya zama daya daga cikin manyan tallafin noma da gwamnatin tarayya ta taba aiwatarwa a yankin.
Kayan da aka raba a kashin farko sun haɗa da:
Injin ban-ruwa – 5,500
Ramin ban-ruwa (Tube Wells) – 5,500
Na’urar dasa iri ta hannu – 1,450
Mini tillers na 7.5HP – 20
Hand tractors na 12HP – 20
Normant Harrows 18HP – 20
Harrows don 12HP – 20
Harkar Fesa maganin kwari – 1,450
Babura – 165
Keke Napep – 165
Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano
An zabi rabon kayan ne domin ƙara yawan amfanin gona, tallafawa kananan manoma, ƙarfafa amfani da injuna yayin noma, tare da inganta zirga-zirga a kauyuka.
Sauran tsare-tsaren da ke cikin babban shirin bunkasa Noma rani sun haɗa da:
Gyaran manyan dam-dam guda uku domin samun ruwa duk shekara
Buɗe sabbin chanal-chanal domin ban-ruwa
Gina hanyoyin kauyuka don sauƙaƙa jigilar kayayyaki
Sanata Kawu ya ce shirin zai taimaka wajen rage fatara da magance rashin tsaro ta hanyar ƙarfafa sana’o’in dogaro da kai da inganta tattalin arzikin yankin. Ya tabbatar da cewa Kashi na biyu, Dana uku dana hudu na rabon kayan za a ci gaba nan gaba kaɗan.
Ya gode wa ofishin kula da harkokin muhalli (Ecology Office) ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Ndako da ke karkashin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), wadda ta tsara kuma ke lura da aikin. Haka kuma ya gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon bayan da ya bai wa shirin.
A nasa bangaren, Sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume ya yaba da tallafin Sanata Kawu , inda ya ce zai sanar da Shugaban Kasa cigaban da aka samu a karkashin wannan shirin da Sanata Kawu da Hon. Rurum suka jagoranta.