Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana kira da gwamnatin jihar ta yi na a kama shi bisa zargin yin kalaman kafa Hukumar Hisbah Mai zaman kanta a jihar a matsayin abin da bai da tushe, kuma nuna rashin iya gwamnati.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, ya sa hannu, Dr Ganduje ya ce wannan kira da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi “salo ne na ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin tsaro da ke ta ta’azzara a fadin jihar.”
Gwamnatin Kano ta nemi a kama Ganduje da Barau
Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta gaza sauke nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, inda ya zargi Gwamna Yusuf da rashin nuna kulawa ga al’ummomin da ke fama da matsalolin tsaro a yankuna irin su Bagwai, Shanono da Tsanyawa.

“Maimakon gwamnati ta mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke addabar jama’a, amma gwamnan ya na son karkatar da hankalin mutane kan gazawarsa. Har yanzu bai kai ziyarar jajantawa ga mutanen da abin ya shafa ba.” Inji Ganduje
Sanata Barau ya mayarwa da Gwamnatin Kano Martani
Sanarwar ta kara da cewa Dr Ganduje ba shi da wata alaka da tashin hankali ko wani aiki da ka iya tayar da hankalin jama’a, kana ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta samar da zaman lafiya na tsawon shekaru takwas ba tare da wata tangarda ba.
Sanarwar ta kuma shawarci Gwamna Yusuf da ya mayar da hankali kan nauyin da kundin tsarin mulki ya dora masa na kare rayuwar jama’ar Kano, maimakon “yin wasan kwaikwayo na siyasa da yawan zargin da ba su da tushe.”