Sojojin Najeriya sun ceto mutane 7 da aka yi garkuwa da su a Kano

Date:

Sojojin Rundunar Operation MESA da ke ƙarƙashin runduna ta 3 ta sojojin Najeriya sun kubutar da mutane bakwai da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a ƙauyen ‘Yankamaye Cikin Gari da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar a ranar Lahadi, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren 29 ga Nuwamba.

Zubairu ya ce sojoji sun samu kiran gaggawa cewa wani ayarin ‘yan bindiga da ke tafiya a ƙafa sun kutsa cikin ƙauyen, inda suka yi awon gaba da mutum 10 tare da kashe wata mata mai shekaru 60.

InShot 20250309 102512486

Yace da samun rahoton, rundunar hadin gwiwa ta sojoji da ‘yan sanda ta nufi yankin, inda suka bi sawun maharan zuwa hanyar Rimaye.

A cewarsa, sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu barin wasu mutum bakwai da suka yi garkuwa da su, waɗanda aka kubutar ba tare da rauni ba.

“Yan bindigar sun tsere ne zuwa Karamar Hukumar Kankia da ke jihar Katsina, kuma ana ci gaba da bin diddigin su,” in ji shi.

Kyaftin Zubairu ya ruwaito kwamandan runduna ta 3 ta sojojin Nigeria ya yabawa da jarunta, hanzari da ƙwarewar sojojin da suka gudanar da aikin.

Ya kuma roƙi al’ummar Kano da su ci gaba da ba da goyon baya ta hanyar ba da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...