Rundunar ’Yan Sandan Kano ta fitar da sabbin dokoki ga masu babura da adaidaita sahu

Date:

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa zata tabbatar da sake jaddada dokar da ta haramta ɗaukar fasinja a kan kowane irin babur, tare da takaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Dokar, wadda Gwamnatin Jihar Kano ta riga ta sanar da ita tun a baya, ta shafi wasu kananan hukumomi da suka haɗa da: Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso, Ungogo (yankin Jido) da Dawakin Kudu (Tambuwal, Gurjiya da Jido).

Hakan n kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Kadaura24.

Rundunar ta ce an baiwa tawagar jami’an tsaro ikon kama wa da bincikar duk wanda ya karya wannan umarni, tare da magance yada bayanan bogi da ka iya tayar da hankalin jama’a.

InShot 20250309 102512486

Ta kuma nuna cewa matakan an ɗauke su ne domin ƙara tabbatar da tsaro a fadin jihar, sannan duk wanda aka samu yana keta dokar zai fuskanci hukunci.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci al’umma da su bi ka’idojin, tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargin ka iya tada hankalin al’umma ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ta layukan gaggawa na rundunar.

Ganduje ya mayarwa da gwamantin Kano martani

Rundunar ta ce zata yi aiki tare da hukumar KAROTA domin tabbatar da cikakken bin doka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...