Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai tantance tare da bibiyar aiyukan Kungiyoyin farar hula da masu zamani kansu a jihar don tsaftace aiyukan na su.
Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Umar Faruq Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a ofishinsa.

Ya ce an dorawa kwamitin alhakin tantance aiyukan dukkanin Kungiyoyin masu zaman kasansu a fadin jihar Kano.
Sakataren Gwamnatin ya ce aiyukan kwamitin sun hadar da lalubo hanyoyi da Kungiyoyin suke samun kudadensu da yadda suke gudanar da aikinsu da kuma inda suke gudanar da aikinsu.
Matsalar tsaro: Gwamna Kano ya kafa Kwamitin karta-kwana
Sannan an dorawa kwamitin alhakin ba da shawarar yadda gwamnati za ta samar da wani tsari na kula da aiyukan Kungiyoyin a Kano.
Ya ce an dorawa kwamitin alhakin rufe ofishin duk wata kungiya da bai yadda da yadda take gudanar da aiyukanta ba.
Kwamitin dai ya kunshi jami’an gwamnatin Kano da wakilan hukumomin tsaro da na Kungiyoyi masu zaman kasansu da wakilan ma’aikatun da ake gani suna da alaka da aikin.
Da yake jawabin karbar kama aiki shugaban kwamitin, kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya ba da tabbacin kwamitin zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da adalci ga kowa don cigaban jihar Kano.