Ministan Jinkai da ba da Agajin Gaggawa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa bayan samun amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jam’iyyar a wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis.
An dai zabi Yilwatda domin maye garubin Ganduje ne a fadar shugaban kasa yayin taron kwamitin kolin na jam’iyyar APC na kasa.
Tuni dai an rantsar da Sabon shugaban Rikon jam’iyyar APC a gaban shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.

Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar ke shirin sake Shirin tunkarar babban zaben 2027.
Ana sa ran cewa Farfesa Nentawe, wanda ya taba tsayawa takarar gwamna a Filato a 2023, zai kawo sabbin dabaru da hadin kai a cikin jam’iyyar domin karfafa martabarta da kawar da rikice-rikicen cikin gida da ke barazana ga hadin kan APC.
Da dumi-dumi: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a kwanakin baya ne tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar a rankansa , kuma ya ce ya yi hakan ne domin ya Sami samar Kula da lafiyarsa