Daga Kamal Yakubu Ali
Hadaddiyar Kungiyar yan Kasuwar jihar kano ta nada Alhaji Munzali Sani Musa a matsayin uban kungiyar bayan rasuwar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata Wanda ya kasance shine uban kungiyar a lokacin da yake Raye.
Shugaban kungiyar Alhaji Auwalu Jakada Gabari yace sun zabi Alhaji Munzali Sani Musa ne bisa la’akari da yadda ya ke tallafawa harkokin kasuwanci da yan kasuwa manya da kuma kanana a bangarori da dama, wanda hakanne ta sa suka bashi wannan matsayi domin samun damar cigaba da yiwa al’umma hidima.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya Kadaura24 t rawaito hadaddiyar Kungiyar ta bayyana Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai Khadimun Nabiyyi a matsayin uban kungiyar inda daga bisani ya ajiye mukamin bisa radin kansa.
Shi dai Alhaji Munzali Sani Musa ya kasance babban Dan kasuwa wanda yake gudanarda harkokin kasuwancinsa a ciki da wajan kasarnan, wanda kuma Aminine ga Alhaji Kabiru Sani Kwangila yakasai SKY khadimun Nabiyyi .
Da dumi-dumi: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria
Da yake jawabi Alhaji Munzali Sani Musa ya ce wannan matsayi da aka dora masa, ba nasa shi ba ne shi kadai, kuma ya Sha alwashin aikin aiki tukuru bisa Gaskiya da adakci don cigaban Kasuwanci a jihar kano .
Ya kuma bukaci sauran mawadata dake jihar kano dasu hada kai domin kara inganta harkokin kasuwanci da tallafawa yan kasuwa a matakai daban daban
Taron ya gudana a farfajiyar gidan Alhaji munzali sani musa dake rukunun gidajen Nasarawa dake lugard.