Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamitin mai mutane 21 domin samar da zaman lafiya da inganta rayuwar matasan jihar Kano, da nufin magance miyagun laifuka da kuma inganta zaman lafiyar al’umma a jihar.
Da yake jawabi yayin kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati dake Kano, Gwamna Yusuf ya dorawa kwamitin alhakin hada kai da jami’an tsaro domin yakar matsalar satar waya da badan daba da shaye-shayen miyagun kwayoyi da ke barazana ga lafiyar jama’a.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 a ranar alhamis, Gwamna Yusuf ya nuna damuwarsa kan yadda aikata miyagun laifuka suka yawaita a lokacin mulkinsa.

Ya yi nuni da cewa, watan farko na hawansa mulki lamarin ya ragu sosai, amma a baya-bayan nan matsalar ta sake dawowa sosai.
Gwamnan ya bukaci kwamitin da ya bullo da tsare-tsaren da za su magance matsalolin da matasa suke fuskanta, ta hanyar ba da shawarwarin, yadda za a koyawa matasan sana’o’i da samar musu da ayyukan yi.
Kungiyar ma’aikatan hukumar kula da kananan hukumomin Nigeria ta yabawa Gwamnan Kano
Ya kuma bukace su da su hada hannu da kungiyoyi da masu hannu da shuni don bunkasa wadannan kokarin.
An dora wa kwamitin alhakin shirya tarukan sasantawa da wayar da kan jama’a kan illolin aikata laifuka, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da tashe-tashen hankula a cikin al’umma, da gano matakan da za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin da aka kaddamar, kwamishinan kimiyya, fasaha, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya godewa gwamnan bisa wannan dama da ya ba shi tare da tabbatar masa da kudirin kwamitin na cimma manufofinsa.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Muhammad Inuwa Idris, kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman; Ibrahim Abdullahi Wayya, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida; Dokta Danyaro Ali Yakasai, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da ci gaban zamantakewa; AVM Ibrahim Umar (Rtd), Darakta Janar na Ayyuka na Musamman, Kano; Amb. Shehu Rabiu, Kwamanda Janar, na Kungiyoyin ‘yan Vigillante, sai Muhammad Sunusi Balarabe da Mamuda Ali Yakasai, shugabannin kungiyoyin ‘yan banga; da Faisal Mahmud Kabir, Manajan Daraktan KAROTA.
Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da Tirela ta yi haɗari a Kano
Sakatarorin kwamatin sun hada da Dan Asabe Yahya, babban sakatare na ma’aikatar tsaron cikin gida da ayyuka na musamman (Sakataren I); Abba Adamu Danguguwa, Babban Sakatare, Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙira (Sakataren II); da Yusuf Dahiru, Daraktan Ayyuka, Ma’aikatar Tsaro da Ayyuka na Musamman (Sakataren III).
Sauran mambobin da ke wakiltar cibiyoyi daban-daban sun hada da Majalisar Masarautar Kano, Malaman addini (Ulama), Rundunar ‘yan sandan Najeriya, Rundunar Sojin Nijeriya, Hukumar DSS, Hukumar Tsaro da Tsaron Jama’a (NSCDC), Hukumar Shari’a, Hukumar Kula da gyaran hali ta Kasa, da Hukumar kuma da shige da fice ta Nijeriya.