Waiya ya kaddamar da kungiyar wadanda za su rika tallata aiyukan gwamnatin Kano a Instagram

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kungiyar yan Kwankwasiyya wadanda za su rika tallata aiyukan gwamnatin Kano ta gwamna Abba Kabir Yusuf ta manhajar Instagram.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya jagorancin kaddamar da kungiyar a ofishinsa ranar talata.

Kwamared Waiya ya ce an kaddamar da kwamitin ne duba da irin tasirin da manhajar Instagram ta ke da shi a gurin al’umma da kuma taimakawa matasa masu amfani da shafin don samar musu da abin yi .

InShot 20250115 195118875
Talla

“Na farko wadannan mutane za su tallata ayyukan gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan kuma an samar masu aikin yi, kun ga mun jefi tsuntsu biyu sa dotse daya”.

Ya ce za su hada kai da kwararru a fannin fasahar zamani domin su ba su horo na musamman domin su san damarun isar da sako a manhajar ta Instagram.

Da take jawabi sabuwar shugabar kungiyar Jamila Auwal Koki ta godewa kwamishinan, sannan ya ba da tabbacin za su yi aiki tukuru domin tallata aiyukan gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Gwamnatin Kano ta Sanya Ranar Rufe Makarantun Firamare da Sakandire

Ta ce “Tabbas Gwamnatin jihar Kano tana aikin da ya kamata, mu kuma za su tsaya tsayin taka domin tallatawa da kuma wayar da akan al’umma kan manufofin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...