Da dumi-dumi: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NPL, ya rage farashin man fetur a karo na biyu cikin mako guda.

Kamfanin man na NNPCL ya dawo da farashin man fetur Naira 890 daga Naira 895, wanda hakan ya nuna kamfanin ya rage Naira 5 a kowace lita.

InShot 20250309 102512486
Talla

Gidajen Mai na NNPCL da ke kan titin Kubwa , Gwarimpa, Wuse Zone 4, da sauran su dake Abuja, sun Fara sayar da man a sabon farashin.

Gwamnatin Kano za ta gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a

Ragin Kudin man fetur din ya zo ne mako guda bayan kamfanin ya Ragewa dillalan kudin yadda suke sayan man a baya.

Yayin da gidajen man NNPCL ke sayar da man a kan Naira 890 kan kowace lita, su kuwa gidajen man dake huldar Kasuwanci da matatar Dangote, irin su AP Ardova, Optima, MRS, da Bovas, suna sayar da man a kan N885 kowace lita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...