Daga: Ibrahim Sidi Mohammad Jega
Sarkin Kabin Jega, Alhaji Muhammad Arzika Bawa, ya bukaci al’umma da su rungumi harkar kasuwanci da gaske domin albarkar da ke cikinta wajen kawo daukaka da ci gaba.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kamfanin kayan aikin gine-gine da manyan motocin ayyukan hanya da za a rika bayarwa haya ga jama’a a jihar Kebbi.

Sarkin Kabin Jega ya bayyana farin cikinsa ganin cewa mamallakin wannan kamfanin Alhaji Lawali Ibrahim Dan Aggo dan asalin Jega ne, yana mai cewa ba abin mamaki bane domin Jega na daga cikin garuruwan da su ka yi fice wajen ilimi da harkokin kasuwanci.
A karshe, ya bukaci al’umma daga matakin jiha zuwa na kasa da su yi amfani da damar da suke da ita wajen kawo ci gaba a Jega.
Kotua a Kano ta yankewa G-Fresh hukuncin zaman gidan yari
A nasa jawabin, dan kwangila, dan siyasa kuma mataimakin shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kebbi, Alhaji Muntari Ahmad Sarki Jega, ya yaba da wannan gagarumin yunkuri.
Ya ce kamfanin zai taimaka sosai wajen ayyukan raya kasa da jin dadin jama’a, musamman ganin yadda ayyukan gine-gine ke qaruwa a Jega, ciki har da aikin tagwayen hanyoyi da gwamnatin jiha ta shirya farayi nan ba da jimawa ba.
Da dumi-dumi: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria
Ya kuma gode wa manyan baki da suka halarci taron ciki har da Alhaji Yusuf Dan Ubangari Shugaban ’Yan Kasuwa Alhaji Murtala Wali da Manajojin Dan Aggo & Sons: Alhaji Buhari Sani da Alhaji Babangida Dan Aggo.
Shugaban karamar hukumar Jega, Alhaji Shehu Umar SK, ya bayyana gamsuwarsa da kafuwar wannan kamfani irinsa na farko a fadin jihar Kebbi. Ya ce kokarin da Alhaji Lawali Dan Aggo ke yi wajen gina matasa a masana’antunsa na Kano, Nasarawa da Jega ya taimaka matuka wajen kawar da zaman banza da samar da ayyukan yi.
Ya yi addu’ar fatan alkhairi ga mai kamfanin da kuma Sarkin Kabin Jega, tare da kira ga masu kula da kamfanin da su rike amana da gaskiya.
Taron kaddamarwar ya samu halartar manyan mutane daga sassa daban-daban da suka hada da ’yan kasuwa, ’yan siyasa, da jami’an gwamnati.