Kano Pillars tayi Wasanni 10 a Jere ba tare da Rashin Nasara ba

Date:

Zaharadeen saleh

Kungiyar kwallon kafa ta kano pillars tayi wasanin guda 10 a jere ba tare data yi rashin nasara ba a gasar cin kofin kwallon kafa ajin firimiya ta Nigeria ta kakar wasa ta 2020/2021.

Kungiyar kano pillars din tayi wasa 10 ne a jere bayan data buga canjaros a wasan data fafata da kungiyar kwallon kafa ta Plateau united, a filin wasa na garin jos dake jihar plateau, zagayen mako na 24 da aka shiga a lahadin nan.

Yanzu haka bisa wannan canjaros da kano pillars ta buga tana matsayi na biyu da maki 45 bayan da kungiyar Akwa united ta dawo matsayi na daya da maki 45 bayan da ta samu nasarar doke kungiyar Kwara united daci biyu da daya.

Ga sakamakon ragowar wasanin da aka buga na zagayen wasa mako na 24 a gasar 2020/2021 NPFL.

Enyimba Fc 0 v Heartland 0

Nasarawa utd 1 v Adamawa utd 0

Katsina utd 1 v warri wolves 0

Lobi Stars 2 v Sunshine fc 1

MFM Fc 1 v Dakkada fc 0

Fc Ifeanyi ubah 0 v Rangers fc 0

84 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...