Daga Aisha Ahmad Dorayi
Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Alh. Auwal Lawan Shu’aibu ya bayyana cewa ya Zama wajibi kowanne Mai unguwa a Karamar Hukumar idan an sayi fili ko Gida a yankinsa ya sanar da Dagacin Wannan yanki domin kyautata al’amuran tsaro a yankin.
Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana hakan ne Yayin wata ganawa da sukai da Masu Unguwannin yankin domin cigaban tsaron Karamar Hukumar.
Auwal Lawan yace Saboda yadda ake samun Shigowar Baki jihar nan akwai bukatar a Dauki irin wadannan Matakai domin sanin da suwa ake mu’amala.
Yace ya Zama wajibi Mai unguwa ya sanar da Dagaci irin Cinikin da aka Yi a yankinsa Koda kuwa Cinikin karamine
“mun Dauki Wannan Matakinne don Inganta Tsaro ba don mu musgunawa kowa ba, Kuma ai idan ka Sami abun da zaka samu ta tsaftacetacciyar hanya Yama fi kaci kudinka ba tare da Rashin hankali ko Kuma kasa Rayuwar al’umma Cikin hadari”. Aranposu
Shugaban Karamar Hukumar ta Nasarawa ya Kuma ce Suma dillalai Masu bada hayar Gidaje akwai tsari da akai domin kyautata sana’arsu.
“Mun Samar da form Wanda za’a Rika baiwa duk Wanda yazo domin kama haya , Wanda a Cikinsa Mai unguwa da dagaci zasu da hannun, Sannan Kuma shi ma Mai kama hayar sai ya Kawo Wanda Zai tsaya Masa”. Inji Aranposu
Alhaji Auwal Lawan Shu’aibu ya bada tabbacin Karamar Hukumar zata Hukunta duk Wanda aka samu da Karya Dokokin da aka gidaya.
Suma Masu Unguwannin sun bada tabbacin bada hadin Kan da ake fada domin kyautata al’amuran tsaro a Karamar Hukumar ta Nasarawa.