Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin cewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka na kwace fili da rushe ginin asibitin zamani da kamfanin Tiamin Multi Services Global Limited ke ginawa a unguwar Gyadi-Gyadi, karamar hukumar Tarauni, ya sabawa doka.
Kotun ta umarci gwamnatin jihar da ta biya kamfanin diyya da ta kai Naira biliyan 2.635 sakamakon wannan take hakki.

A cewar bayanan kotu, gwamnatin da ta gabata a karkashin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta kwace filin tare da rushe gine-ginen da aka kusa kammalawa a wancan lokaci.
Kamfanin Tiamin ya shigar da kara tun a watan Oktoba na shekarar 2019, yana neman diyya kan abin da ya bayyana a matsayin take hakkin mallaka da rushe asibitinsa ba tare da bin ka’idojin doka ba.
A hukuncin da Mai shari’a Ibrahim Karaye ya yanke a ranar Laraba, kotun ta bayyana cewa kwace filin da gwamnatin Kano ta yi a ranar 3 ga Satumba, 2021, ta hanyar wasika daga Hukumar Kula da Filaye ta Jihar Kano, ya saba da kundin tsarin mulki da kuma dokar mallakar fili ta ƙasa (Land Use Act).
Mai shari’a Karaye ya jaddada cewa gwamnatin jihar ta dauki matakin ne ba tare da bai wa kamfanin damar kare kansa ba, lamarin da ya sa kwace filin da kuma rushe ginin suka zama babu inganci a idon doka.
Kotun ta kuma soki gwamnatin jihar bisa matakin rushe ginin yayin da karar ke gaban kotu, tana mai bayyana hakan a matsayin saba wa doka da kuma abin kyama.