Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau ta ce za ta shiga sabuwar haɗakar ƴan hamayya ta National Coalition Group ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark domin tunkarar zaɓen 2027.

A wata sanarwar bayan taron da ƙungiyar ta yi ranar Alhamis, ND ta ce duk da amincewar da ta yi na shiga haɗaka, amma za su ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tattaunawa yiwuwar kafa sabuwar jam’iyya ko kuma shiga wata jam’iyyar domin yin tafiya tare.
Harwayau, ƙungiyar ta Northern Democrats ta ƙara da cewa sun amince da matsa wa gwamnati lamba musamman jagorancin majalisar dokoki wajen ganin an tabbatar da bin tsarin mulkin ƙasar sau da ƙafa.
Daga ƙarshe ƙungiyar ta ce mambobinta sun amince su tattauna da jihohin arewacin ƙasar 19 dangane da halin-ko-in-kula da ake ciki dangane da yanayin da yankin yake ciki da suka haɗa da talauci, rashin aikin yi da rashin tsaro