Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware kudi domin sake gina masallacin da wani mutum ya bankawa wasu masallata wuta yayin da suke sallar asuba a karamar hukumar Gezawa.
A wata sanarwa da jami’in yada labaran yankin Jamilu Mustapha Yakasai ya aikowa Kadaura24, ya ce Shugaban karamar hukumar Gezawa, Alhaji Mukaddas Bala Jogana, ya bayyana cewa, baya ga sake gina masallacin, gwamnatin za ta kuma gina ajujuwa, da bandakuna, da rijiyar burtsatde a harabar masallacin.

Mukaddas ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kammala aikin titin kilomita 5 na karamar hukumar.
Hukumar shari’a ta Kano ta ladaftar da wasu ma’aikatan kotu
Ya yi kira ga ma’aikatar ayyuka da ta fara aikin titin Dan Madanho zuwa Kwasangwami zuwa Zango, wadda ya ce hanya ce mai muhimmanci da al’umma da dama ke amfani da ita.
Alhaji Mukaddas Bala ya nuna matukar godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kokarinsa na daukaka martabar jihar Kano. Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da marawa gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf baya.
Shugaban karamar hukumar Gezawan ya yi alkawarin za’a ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa don amfanin al’ummar yankin, musamman a fannonin kiwon lafiya, ilimi, da sauransu.