Daga Usman Hamza
Hukumar Kula da Harkokin shari’a ta Jihar Kano wato Kano State judicial service commission JSC, a taronta na 82 da aka gudanar a ranar 20 ga Watan Mayu,2025, sun amince da jerin Wadansu matakan ladabtarwa da hukunce-hukunce a yunkurin ta na ganin Cewa ta sauke Nauyin da Doka ta dora mata na dawo da da’a da kimar da Bangaren yake dashi a idanun Duniya.
Hukumar ta dauki shawarwarin kwamitin bincike da ladaftarwa na (JPCC) a cikin korafe korafen da aka Gabatar gabansa akan Wadansu Ma’aikata Daban dabam.

An ragewa Magatakarda Salisu Sule matakin girma Daya bayan da Kwamitin JPCC ya samu rinjayen shaidun akan korafe korafe guda 4 da Mutane Daban dabam Suka rubuta da Suka tabbatar da Cewa ya aikata Laifukan da basu dace ba game da zagi da tsoratarwa da cin zarafin ofis.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Kotun Kano Baba Jibo Ibrahim ya aikowa Kadaura24,ya ce Binciken da aka Gudanar ya nuna cewa a gurare da dama ya kanyi amfani da sunan Judiciary ya na cin zarafi da tsoratar da jama’a yayin aikinsa.
Hukumar ta lura cewa a baya an bashi wasiƙar gargadi a ranar 19 ga Disamba 2024 shine kuma yanzu aka yanke shawarar daukar wannan matsayi tare da aiwatar da matakin farko.
A cikin wani binciken Kuma na daban Kwamitin na JPCC ya samu Ahmad Aliyu Dan maraya da Laifin yin jebun Takardar affidavit da buga sitamfin High Court da kuma buga hatimin rantsuwa.
Hukumar ta amince da shawarwarin Kwamitin JPCC Sannan aka umarce shi a kan yin ritayar dole sakamakon samunsa kai tsaye da yin rashin gaskiya.
A cikin wata shawara ta Daban da Kwamitin na JPCC ta bayar, hukumar Kula da Harkokin shari’a ta Jihar Kano JSC ta amince da Dakatar da Alkali Mustapha Kiru na kotun shari’ar Musulunci Daga yin shari’a har tsawon shekara Daya bayan Kwamitin na JPCC ya sameshi da yin wani kwarya kwaryan Hukunci da rufe Wata Shari’a Mai lamba CV/ 81/2021 tsakanin Zubairu Kiru Da Kabiru Ibrahim Saboda dalilin Rashin Gabatar da shaida da Mai kara baiyiba a kotun. Bayan Kuma ya rufe wannan shari’a Sai ya Bayar Da Takardar Mallaka a Madadin gonar da ake shari’a a kanta Wanda Kuma Hakan ya Nuna a fili Cewa ya saba da ka’idar aiki da Kuma Adalcin shari’a na damar sauraro. Sannan bugu da Kari shidai wannan Alkali ya garkame shi Mai korafi a gidan gyaran tarbiya har tsawon sati 3 ba tare da daftarin shari’a ba Saboda kawai ya Nemi bahasi akan Bayar Da Takardar Mallaka da Alkalin Yayi ga Wanda Ake zargi.
Haka Kuma Kwamitin na JPCC ya Bayar Da Tallafi gargadi ga Alkali Nasiru Ahmad bayan Kwamitin ya sameshi da yin sakaci a Wata Shari’a Mai lamba CR/319/2022 tsakanin kwamishinan Yan Sanda da Auwal Sani da Mutane 3 da kuma nassoshi na aikatawa wanda zai iya haifar da rashin adalci.
A cikin tsare tsarenta na Samar Da Ci Gaba tare da kokarin kula da horo hukumar ta JSC ta Kuma sake Bayar da Takardar gargadi ga Alkalin Majistare Sakina Aminu akan Wata Shari’a Dake tsakanin kwamishinan Yan Sanda da Isah Hassan Mai lamba KA/0013/CT26/2024 da Kuma Wata Shari’a Dake tsakanin kwamishinan Yan Sanda da Umar Abdullahi Mai lamba KA/004CT26/HK/2025 ta Hanyar yin amfani da Dan sanda a matsayin mai Gabatar da kara Lokacin da take Gudanar da wadannan shara’u . Wanda Hakan Kuma ya saba da umarnin da Cif Joji ko duk Wani Babban Ma’aikaci Wanda yake Gaba da Ita Yayi . Sannan an shawarceta da ta inganta dangantakar ta ta aiki da duk Wani lauyan Gwamnatin da aka turo kotunta Domin yin aiki. Sannan ta tabbatar ta Yi Biyayya da umarnin da Cif Joji ta bayar na haramta yin amfani da Yan Sanda a matsayin Masu Gabatar da kara a kotun ta.
A Wata Samuwa Kuma hukumar ta amince da janyewar dakatarwan da akayi Wa Babban Majistate Mustapha Sa’ad Datti da Kuma Alkalin Majistare Rabi Abdulkadir Waɗanda a kwanakin baya aka Dakatar Dasu Daga yin shari’a. To Bayan Kyakkyawan nazari da kididdigewa hukumar ta JSC ta yanke shawarar cewa ya kamata su ci gaba da zama a Kotu Domin yin shari’a Sannan kuma su ci gaba da yin hukunce-hukuncen shari’a. An Kuma yi masu tuni da su tabbatar da bin mafi girman ka’idodi na aminci da ƙwazo a cikin Gudanar da ayyukan hukunce-hukuncen shari’a.
Hukumar Kula da Harkokin shari’a ta Jihar Kano ta kasance mai dagewa a matsayin ci gaba da yin lissafi da kwarewa a cikin bangaren Gudanar da aikinta tare da jajircewa da yin tsayuwar daka ga Kowane nau’i na rashin Adalci.