Kungiyar kafafen yada labaran yanar gizo ta bukaci gwamnatin Kano ta gyara hanyoyin dake karkara

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kungiyar kafafen yada labarai na yanar gizo a Kano ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta mai da hankali wajen samarwa da gina sabbin hanyoyi a yankunan karkara domin inganta rayuwar mazauna yankunan.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar bayan taron da wadda shugaban kungiyar Abubakar Abdulkadir Dangambo da sakataren kungiyar Isyaku Ahmad su ka sanyawa hannu kuma suka turowa kadaura24, bayan kammala babban taron ya’yan kungiyar na farko tun bayan kafa sabuwar kungiyar wacce ta ke karkashin uwar kungiyar yan jaridu ta kasan NUJ.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sanarwa ta cegyara hanyoyi karkara zai taimaka sosai wajen ingantawa rayuwar mazauna yankunan, tare da ba su damar fitar da kayan gona da suke nomawa a gonakinsu cikin sauki wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikinsu.

Gwamnatin Kano za ta sake gina Masallacin da aka kona a Gezawa

Haka zalika, sanarwar ta kuma bukaci gwamnatin jihar Kano da ta tallafawa Manoman jihar da abubuwan da suke bukata sakamakon gabatowar daminar bana.

“Akwai abubuwa da dama da manoma suke bukata musamman a farkon damina, wanda hakan zai taimakawa manoman don sun sami amfanin gona mai tarin yawa”. Inji sanarwar

InShot 20250309 102403344

Sanarwar ya ce nan ba da jimawa kungiyar za ta fara yiwa sabbin mambobinta rijista akan kudi Naira dubu 25.

Sanarwar ta ce an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi cigaban kungiyar da kuma aikin jarida da jihar Kano baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...