Daga Abubakar Sa’eed
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi Yan Siyasa da Yan takara da su guji sa a Daga Hotunan su a taron Ranar Damokaradiyya ta bana da za’a gudanar Ranar Asabar.
Ganduje ya bayyana hakan ne Yayin Bikin baiwa Matasa da Dalibai Motoci domin bunkasa harkokin su.
Ganduje yace ba zai lamunci Yan Siyasa su Rika sawa ana Daga Hotunan su a Yayin taron Ranar Damokaradiyya ba Saboda akwai Manyan Baki da zasu Shigo jihar nan.
“Duk Dan takarar da ya baiwa Matasa Kayan maye ko Makami suka shiga dasu wajen taron mu to da kaina Zan sa a Kama yaron, Sannan Kuma Zan yi Maganin Wanda ya basu”. Inji Ganduje
Yace Shugaban jam’iyyar APC na Kasa da sauran Shugabanin jam’iyyar Za su halarci wajen taron na Ranar Damokaradiyya ta bana.
Gwamna Ganduje yace bayan Sunan Shugaban Kasa Muhd Buhari da Sunan Shugaban jam’iyyar APC na Kasa dana Gwamna Kano bama so muji an kirawo Sunan Wani Dantakara.