Daga Mubarak Ibrahim
Wata kotun majistare da ke Kano ta saurari karar tsohon kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na Kano, Muaz Magaji, wanda ya “rasa jinsa” bayan wani hatsarin da yayi Sakamakon bin da ‘yan sanda suka yi Masa a Abuja a ranar Alhamis.
Kadaura24 ta rawaito an kama Muaz Magaji ne bayan ya Kasa sarrafa motarsa tare da afwa fitilar wutar titi.
Da ya bayyana a gaban Alkalin Aminu Gabari a ranar Juma’a, Lauyan Magaji, Garzali Ahmad, ya ce wanda yake karewa ya rasa jinsa na dan wani lokaci sakamakon raunin da ya samu bayan hatsarin da yayi.
Barr. Ahmad ya kara da cewa wanda ake tuhumar ba zai iya sauraron tuhumar da ake yi masa ba kuma har ya amsa tuhumar.
Don haka ya roki kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa domin neman lafiyarsa.
Da yake yanke hukunci kan lamarin, Mai Shari’a Aminu Gabari ya ba da umarnin a kai Muaz Magaji asibitin ‘yan sanda kuma ya ci gaba da zama a hannun ‘yan sandan.
Ya dage sauraron karar zuwa ranar Litinin 31 ga watan Janairu.