An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Date:

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta da tsakanin jama’a ya bayyana cewa an dauke fitaccen malamin addini, Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, daga gidan yarin Kurmawa da ke Kano zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Wata majiyar kusa da iyalan malamin ta shaida wa Kadaura24 cewa, daga baya suka ji rade-radin cewa an kai shi gidan yarin Kuje da ke Abuja, lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin mabiyansa da ‘yan uwa.

A wata sanarwa da Askia Nasiru Kabara ya fitar a madadin iyalan Shaikh Abduljabbar, ya ce suna zargin akwai manufar siyasa ko wata bakar manufa a bayan daukar malamin daga Kurmawa zuwa wani wuri daban, musamman a wannan lokaci da ake samun sabbin jita-jita kan batun da ya shafi Shaikh ɗin.

“Mun sani hukumar kula da gidajen yari ta kasa tana da ikon mayar da fursuna duk inda ta ga dama, amma abin mamaki shi ne me ya sa sai yanzu aka dauke shi bayan shekaru hudu da yake a Kurmawa?” in ji Askia.

Ya kara da cewa, tun bayan barkewar maganar Lawan Triumph, an fara yada jita-jitar cewa za a saki Shaikh Abduljabbar, wanda hakan ya jawo cece-kuce daga bangaren kungiyar Izala.

Iyalan Shaikh din sun bayyana damuwarsu cewa yanzu da aka ce an mayar da shi Abuja, ba su da tabbacin yadda ake kula da shi, musamman wajen abinci da lafiya, domin kafin yanzu suna kai masa abinci daga gida.

A karshe, iyalan sun bukaci manyan jami’an gwamnati da hukumomi su sanya ido a cikin lamarin, ciki har da:

1. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

2. Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

3. Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu

4. Sufeton ‘yan sanda na kasa (IGP)

5. Daraktan DSS

6. Gwamnatin jihar Kano

7. Da kungiyoyin kare hakkin dan adam

“Abin da ya faru da Shaikh Abduljabbar ya zama abin damuwa da ya shafi tsaro da adalci a kasa baki daya. Bai kamata wasu kalilan su yi wasa da rayuwar mutum ba,” in ji sanarwar.

Iyalan sun roki gwamnati da hukumomin tsaro da su binciki lamarin da gaggawa domin tabbatar da cewa ba a tauye masa hakkinsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...