Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Date:

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa yafe masan da shugaban ƙasa ya yi kwanan nan ta ba shi sabuwar dama a harkokin siyasa, inda ya ce watsi da shi da Shugabannin tafiyar Kwankwasiyya su ka yi ne ya sa ya yanke shawarar barin ƙungiyar.

Kadaura24 ta rawaito Farouk Lawan, wanda ya taɓa wakiltar kananan hukumomin Bagwai/Shanono a majalisar ta tarayya, na cikin mutum 175 da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa a ranar 9 ga Oktoba.

An taɓa gurfanar da Lawan a gaban kotu a shekarar 2021, inda aka same shi da laifin cin hanci bayan zargin karɓar kuɗi a 2012 domin cire sunan wani kamfani daga jerin waɗanda aka zarga da hannu a badakalar tallafin man fetur. Bayan kammala zaman gidan yari a Oktoba 2024, ya ce darasin da ya samu a gidan kaso, shi ya canza masa ra’ayi game da siyasa .

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

A wata hira da ya yi da BBC, Faruq Lawan ya bayyana cewa ya yi mamakin watsi da shi da yan tafiyar Kwankwasiyya suka yi duk da dadewarsa yana tare da su.

“Idan Allah Ya jarrabe ka, Yakan kuma bude maka idanu ka gane su waye abokan ka na gaskiya,” in ji shi, yana mai cewa jagoran tafiyar bai taɓa kira ya jajanta masa ba ko da bayan ya fito daga gidan yari.

Ya ƙara da cewa, “Shekara guda kenan da na fito, amma bai kira ni ya jajantamin ba’.”

Lawan ya ce duk da cewa yana cikin jam’iyyar PDP lokacin da yake gidan yari, sai ya umarci magoya bayansa su shiga NNPP a zaben 2023, amma yanzu ya ga jam’iyyar ba ta da tasirin da ya dace da burinsa na siyasa.

“Ya kamata mutum ya shiga jam’iyyar fa zata iya tasiri. Amma NNPP a halin da take yanzu ta yi kankanta a gareni,” in ji shi, yana mai cewa yanzu hankalinsa ya karkata zuwa siyasar kasa gaba ɗaya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...