Muaz magaji ya kurmance, yayin da kotu ta bada Umarnin kai shi Asibiti

Date:

Daga Mubarak Ibrahim
Wata kotun majistare da ke Kano ta saurari karar tsohon kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na Kano, Muaz Magaji, wanda ya “rasa jinsa” bayan wani hatsarin da yayi Sakamakon bin da ‘yan sanda suka yi Masa a Abuja a ranar Alhamis.
Kadaura24 ta rawaito an kama Muaz Magaji ne bayan ya Kasa sarrafa motarsa ​​tare da afwa fitilar wutar titi.
 Da ya bayyana a gaban Alkalin Aminu Gabari a ranar Juma’a, Lauyan Magaji, Garzali Ahmad, ya ce wanda yake karewa ya rasa jinsa na dan wani lokaci sakamakon raunin da ya samu bayan hatsarin da yayi.
 Barr. Ahmad ya kara da cewa wanda ake tuhumar ba zai iya sauraron tuhumar da ake yi masa ba kuma har ya amsa tuhumar.
 Don haka ya roki kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa domin neman lafiyarsa.
 Da yake yanke hukunci kan lamarin, Mai Shari’a Aminu Gabari ya ba da umarnin a kai Muaz Magaji asibitin ‘yan sanda kuma ya ci gaba da zama a hannun ‘yan sandan.
 Ya dage sauraron karar zuwa ranar Litinin 31 ga watan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...