Kungiyar cigaban Ilimi da gyaran tarbiya ta unguwar zango ta shirya taron kan tarbiyya da tsaro

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wani Malami a jami’ar Bayero dake Kano Dr. Murtala Uba Zango ya bayyana cewa dukkanin rukunonin al’umma suna da rawar da za su taka don magance matsalolin fadan daba da suka addabi wasu unguwanni a Birnin Kano.

” Al’ummar unguwannin da ake fada daba kamar su Zango da Zage da Kofar mata da kuma Dorayi suna da gagarumar gudunmawar da za su bayar don magance matsalar, ta hanyar baiwa jami’an tsaro hadin kai da basu bayanan sirri don kawar da matsalar a cikin al’umma”.

InShot 20250309 102512486
Talla

Dr. Murtala Zango ya bayyana hakanne yayin da ya gabatar da lacca Mai taken matsalolin tsaro a unguwannin Zango, Zage, Kofar mata da Dorayi da hanyoyi da za a bi don magance matsalolin, wanda kungiyar Zango Educational Initiative ta shirya.

Malamin ya ce aikin Samar da tsaro ba na gwamnati da jami’an tsaro ba ne kadai, kowa yana da gudunmawar da zai bayar domin kawo karshen matsalar.

Gwamnatin Kano ta sanar da Ranar Fara hutun zangon Karatu na 3 ga ɗaliban jihar

” Masu unguwanni suna da rawar takawa a wannan sabgar haka su ma yan unguwanni sai gwamnatin da kuma Jami’an tsaro, tabbas idan wadannan rukunonin suka ba da ta su gudunmawar Babu shakka za a sami Mafita dangane da matsalolin fadan daba da suka addabi al’umma”. Inji Dr. Murtala Uba zango

Ya yi bayani mai tsaho dangane da rawar da konne rukuni zai taka don magance matsalar, inda ya ce ita tarbiyya ba ta mutum daya ba ce sai kowa ya ba da ta shi gudunmawar don inganta rayuwar matasan da ake fata a gobe su zamo Shugabanni.

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Dr. Bello Yahuza shi ma Malami ne a jami’ar Bayero dake Kano a yayin taron ya gabatar da makala mai taken Ilimin zamani a hanga ta addini musulunci, inda yayi jawabi Sosai dangane da yadda ya kamata al’ummar Musulmi su nemi Ilimin zamani ta yadda ba zai cutar da lahirarsu ba .

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Zango Educational Initiative Dr. Usman Umar Zango Wanda ya ce an yiwa taron ne domin fadakar da al’umma musamman matasa yadda za su kaucewa fadan daba da kuma yadda za su nemi Ilimin zamani ba tare da ya cutar da lahirarsu ba .

Ya kuma godewa dukkanin wadanda suka halarci taron kamar su Masu unguwanni da yan Kungiyoyin daban-daban na matasa Dana mata dake unguwar Zango da kewayenta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Tinubu

  Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya...

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta yi Sabon Shugabanta na Kasa

  Ministan Jinkai da ba da Agajin Gaggawa, Farfesa Nentawe...

Ku shiga harkokin Kasuwanci domin akwai albarka a ciki – Sarkin Kabin Jega ga matasa

Daga: Ibrahim Sidi Mohammad Jega Sarkin Kabin Jega, Alhaji Muhammad...

Kotua a Kano ta yankewa G-Fresh hukuncin zaman gidan yari

Kotu ta aike daAbubakar Ibrahim G. Fresh gidan gyaran...