Gwamnatin jihar Kano za ta yi taron jin ra’ayoyin jama’a da masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen da ake shirin yi a kundin tsarin mulkin ƙasa.
Za a gudanar da taron ne a yau Alhamis da misalin karfe 1 na rana a dakin taro na Coronation Hall da ke fadar gwamnatin Kano.

Ta shirya taron domin fitar da matsayar jihar kafin zaman sauraron ra’ayoyi na majalisar dattawa.
Gwamnatin Kano ta sanar da Ranar Fara hutun zangon Karatu na 3 ga ɗaliban jihar
Sanarwar da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce an gayyaci wakilan majalisar jiha da ta tarayya, kungiyoyin farar hula, kafafen yaɗa labarai, yan kasuwa, shugabannin addini da na gargajiya da kuma ƙungiyoyin kwadago da na sauran ƙwararru.