Daga Samira Hassan
Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan gaba kadan za ta fara shiga lungu da sako na kananan hukumomi 44 domin jiyo ra’ayoyin al’umma game da aikin da su ke bukatar gwamnatin ta yi musu a yankunansu.
” Gwamnan jihar Kano ya samar da wannan ofishin nawa ne don mu rika jiyo abubuwan da al’umma su ke bukata mu kai masa shi kuma ya aiwatar don amfanin al’ummar jihar Kano”.
Sabuwar mai baiwa gwamnan Kano Shawara ta musamman kan fadakar da al’umma, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ce ta bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Kano .

Ta ce yadda gwamnan kano ya shiga cikin al’umma lokacin da ya ke yakin neman zabe , haka su ma za su shiga cikin al’ummar domin su jiyo abubuwan da su ke bukata don aiwatarwa al’ummar jihar .
” Yanzu haka gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya cika sama da kaso 85 na alkawuran da ya yi wa Kanawa lokacin da ya ke neman kuri’un al’umma , don haka yanzu za mu fara jin aiyukan da al’umma suke bukatar sannan mu gabatarwa gwamnan domin zartar da aiyukan”. Inji Bilkisu Indabo
Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa
Mai baiwa gwamnan Shawara wacce it ce tsohuwar Kantomar karamar hukumar Wudil ta ce za ta yi aiki tukuru domin ganin ta sauke nauyin da gwamnan Kano ya dora mata don inganta rayuwar al’umma.
Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta bukaci al’umma jihar Kano su ba ta hadin kan da ya dace don kyautata rayuwar al’ummar jihar Kano dake birni da karkara.