Cin zarafi: Gwamnatin Kano za ta sanya kafar wando da sojojin baka – Kwamared Waiya

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta na yin duk mai yiwuwa domin magance Siyasar cin mutuncin mutane musamman a gidajen Radio dake jihar.

” Tabbas Gwamnan Kano ya damu matuka da wannan abun da ya ke faruwa a Kano, kuma ya dora mana alhakin kawo gyara don ganin ana gudanar da harkokin Siyasa a Kano ba tare da cin zarafi ba”.

Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki a sha’anin yada labarai, wanda hukumar kula da kafafen radio da talabijin ta kasa NBC ta shirya a Kano.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce a kokarinsa na ganin ya magance matsalolin cin zarafin al’umma a kafafen yada labaran musamman Radio, Kwamared Ibrahim Waiya ya ce ya zauna da sojojin baka kuma ya fada musu kudirin gwamnatin Kano, sannna an kafa musu kungiya ta “Gauta Club” domin sanin su waye su ke magana a gidajen Radio da kuma samun bayanan su.

Ya ce sun zauna da sojojin bakan kuma sun sanar da su kudirinsu na tsaftace maganganu a kafafen yada labaran, kuma sun yi alkawarin za su hada hannu da gwamnatin Kano don magance matsalar.

” Tuni mun sanya su na yin rijistar ya’yan kungiyar kuma daga haka ne gwamnatin Kano za ta sami bayanansu da kuma sanin yadda za ta magance matsalar, domin ba za ka iya magance matsala ba idan ba ka santa ko ka san wanda yake aikatata ba” . Kwamishina Waiya

Gwamnan Kano ya Bayyana Matsayarsa Game da Hawan Sallah Karama a Jihar

Ya ce akwai bukatar al’ummar jihar Kano su tashi tsaye domin tallafawa kokarin gwamnatin jihar Kano wajen magance wannan matsala, ta hanyar kyamatar masu cin zarafi al’umma da sunan yankin fadin albarkacin baki.

Ya kuma hori masu gabatar da Shirye-Shiryen Siyasa a gidajen Radio a Kano da su ba da tasu gudunmawar ta hanyar daina ba da damar cin zarafin al’umma.

” Abun mamaki a Kano ne za ka ji mutam yana cin zarafin sarki ko gwamna kawai saboda ya nada Naira dubu 10 , kuma ka ga yana yawo abunsa ba tare da an dauki wani mataki akansa , tabbatas gwamnatin Kano ba zata lamunci wannan dabi’ar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hawan Sallah: Yansandan Kano sun gayyaci hadimin Sarki Sanusi II bayan mutuwar wani

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta...

Barka da Sallah: Gwamnan Kano ya bukaci yan jihar su rungumi zaman lafiya da adalci

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Sarki Aminu da Sarki Sanusi sun bukaci gwamnati ta hukunta duk masu hannu a kisan Mafarautan Kano a Edo

Daga Aliyu Danbala Gwarzo da Sani Idris maiwaya   Mai Martaba...

Murtala Sule Garo ya yiwa Kanawa Barka da Sallah

Ina taya daukacin al’ummar Musulmi maza da mata musamman...