Daga Aliyu Danbala Gwarzo da Sani Idris maiwaya
Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II sun yi kira ga Gwamnati ta tabbatar ta dauki matakin hukunta duk wadanda aka samu da laifin kisan mafarauta yan asalin jihar Kano Wanda akayi a jihar Edo.
Sarakunan sun yi wannan kira ne a sakonsu na Barka da Sallah, tare da jaje da ta’aziyyar rasuwar yan asalin jihar Kano da aka kashe a jihar Edo.
Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Sallah
Sun yi Allah -wadai da kisan sannan su ka yi addu’ar Allah ya jikan mamatan ya kuma gafarta musu ya karbi shadarsu.

Sarkin Kano ya bukaci Gwamnati a kowane mataki da ta samar da hanyoyin saukakawa jama’a sakamakon wahalhalun rayuwa da al’uma ke fama.

A wani sako da sakataren yada labaran Sarki Aminu, Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya ce Aminu Ado Bayero ya sake tunatar da Gwamnati irin nauyin da yake kanta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma lafiyarsu.
Ya bukaci mawadata dake cikin al’uma su cigaba da taimakon da tallafawa marasa karfi domin samun saukin al’amuran rayuwa na yau da kullum.