Ina taya daukacin alβummar Musulmi maza da mata musamman na jiharmu ta Kano mai albarka murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma bikin karamar sallah.
A dai-dai lokacin da muke gudanar da bukuwan karamar sallah kamar yadda aka saba, kada mu manta da muhimman darusan da muka koya cikin watan Ramadan wadanda suka hada da hakuri da yafiya da jin kai da taimakon juna.

Azumin watan Ramadan kamar yadda malamai su kai ta fadarkarwa wani kebantaccen lokaci ne da kan karato da bawa zuwa ga ubangijinsa.
Manufar darusan da ke cikin wannan wata mai alfarma shi ne su ci gaba da wanzuwa cikin alβumma don samun alβumma mai inganci.
Ina kira ga alβummar Musulmi musamman na wannan jiha da su dukufa wajen adduβoβin zaman lafiya da arziki mai dorewa.
Ina yiwa kowa fatan alkairi. Allah ya karbi ibadinmu ya kuma bamu lafiya da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki. Amin. MSG