Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Wani malami a Kano mai suna sharu sani Madigawa ya yabawa Shugaban hukumar ingantuwar aiyukan ta kasa Baffa Babba Dan’agundi Bisa yadda ya dauki yan jihar kano ya basu mukamai daban-daban a Ofishinsa.
” Ina yabawa Baffa Babba Dan’agundi saboda ya yi abun da ya dace na baiwa Matasa mukamai , saboda irin gudunmawar da suka bayar yayin zaɓen da ya gabata, hakan zai karawa matasa kwarin gwiwar shiga Siyasa”.
Sharu Madigawa ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da wakilin jaridar kadaura24.
Rikicin NNPP: Gwamnan Kano ya Bijirewa Umarnin Kwankwaso, na cire wasu jami’an gwamnati
‘ Ina mafani da wannan dama wajen taya Nabila Bature murna Bisa mukamin da Baffan ya bata na wakiliyarsa a Kano ta yadda zata rika sanya idanu akan duk abun da ya shifi yan kungiyoyin Support Group”. Inji sharu madigawa
Ya ce yana da yakinin Nabila Bature zata yi aikin ta yadda ya dace domin ciyar da jam’iyyar APC gaba a jihar kano, da kuma kyautata alaka tsakanin Baffa Babba Dan’agundi da yan kungiyoyin Support Group.
Ya bukace ta da ta zama mai gaskiya da rikon Amana, Sannan ta yi aiki tukuru domin sauke nauyin da Baffa Babba Dan’agundi ya dora mata.