Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Karamar ministar babban birnin tarayya Abuja Dr.Mariya Mahmoud Bunkure Takarbi Lambar yabo matsayin gwarzuwar mace mai kishin Al’ummah da cigaba daga kansilolin Karamar hukumar Bunkure.
Kansilolin sun ce sun Karrama ministar ne saboda irin gagarumar da take bayarwa wajen tallafawa al’umma a Karamar hukumar Bunkure da yankin Rano Kibiya da Bunkure da ma jihar kano baki daya ba.

Lambar yabon da zababbun kansilolin karamar hukumar Bunkure suka Shirya mata kuma suka mika mata ta hannun babban mataimaki a gareta SA. Hon. Abba Kawu Gurjiya ta Isa Gareta a jiya talata.
Hukumar Tace Fina-Fina ta Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Zargin da ake yiwa Jaruma Maryam Yahya
Sai kuma lambar yabon da wata Gidauniyar kiwon lafiya ta bata mai suna AMBIENCE OF HOPE EXEPTIONAL FOUNDATION ta hannun babban mai taimaka mata na musamman SA. Abdullahi Isah Kauranmata.
A lokuta daban-daban ministar ta sami lambobin yabo daga kungiyoyin daban-daban, saboda irin gudunnawa da jajircewa da take yi wajen taimakawa masu karamin karfi a cikin al’umma.