Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya jagoranci taron kaddamar da majalisar zartarwa ta kasa a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Taron wanda aka fara a ranar Litinin, ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, Sen. George Akume, da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, sabbin ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.
Aikin majalisar, dai kamar yadda aka rubuta a cikin Dokar Ma’aikatu da Ayyuka na Ministoci, ita ce ta zama majalisar mai ba da shawara ga shugaban kasa, wanda ke a matsayin shugabanta.
Zan Sauke duk Ministan da ya gaza sauke nauyin da aka dora masa – Tinubu
Majalisar zartarwar na da rawar takawa, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada wajen baiwa shugaban kasa shawarar sanin alkiblar gwamnati, duk da cewa shugaban kasa ne mai yanke hukunci.
Bai Kamata Gwamnatin Kano ta yi Auren Zawarawa a Wannan Lokacin ba – Shitu Sani Marshall
Ita ce majalisar zartarwa ta gwamnatin tarayya kuma tana cikin bangaren zartarwa mai ba da shawara ga shugaban kasa, wanda ke zama shugabanta.
Ana nada membobin majalisar ministocin kuma su kai rahoto ga shugaban kasa.
A kwanakin baya ne Tinubu ya kaddamar da ministoci 45 da za su yi aiki a matsayin ministocinsa. (NAN)