Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

Date:

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA’IB)

Assalamu Alaikum Warahmatullah,

Sakamakon rasuwa da Allah ya yiwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata a Hadaddiyar Daular Larabawa a jiya Juma’a, Majalisar Malamai ta Kasa reshen Jihar Kano tana gayyatar daukacin al’umma domin halartar Sallatul Ga’ib na addu’ar rahama ga mamacin.

InShot 20250309 102512486
Talla

Za a gudanar da Sallatul Ga’ib din a yau, Asabar 28/06/2025, a Masallacin Umar Bin Khattab, dake Dangi, Kano, da misalin karfe 2:00 na rana.

Ana rokon al’umma da su hallarci wannan ibada domin neman rahamar Allah ga mamacin, tare da yi masa addu’ar samun gafara da jinƙai.

Allah ya jikansa, ya sanya Aljannah makomarsa.

Wassalamu Alaikum Warahmatullah.

Sanarwa:
Salisu Umar Gama,
A madadin Shugaban Majalisar Malamai,
Malam Ibrahim Khalil

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...