Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Date:

Daga Mubina Ahmad Galadanchi

Wasu daga cikin al’ummar unguwar unguwa uku da kewaye dake karamar hukumar Tarauni a jihar kano sun koka da yadda karamar sakandiren Maza ta yankin ta zama wurin shaye-shayen miyagun kwayoyi a yayin da daliban makarantar ke tsaka da Karatu .

” Abun takaici yadda makarantar ta lalace wanda hakan ya baiwa yan daba damar shiga makarantar a duk lokacin da su ke so domin yin shaye-shaye ko ajiye Makaman da su ke taa’addanci da su”.

InShot 20250309 102512486
Talla

Da yake zantawa da Jaridar Kadaura24, daya daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar mai suna Ahmad Aminu (Arewa) ya ce Makarantar tana cikin mawuyacin hali, sakamakon lalacewar Azuzuwan Makarantar da kuma rashin Kofar za a rika rufe Makarantar.

“Mafi yawan azuzuwan Makarantar GSS Unguwar uku duk a lalace suke, baya ga rashin kujerun zama na ɗalibai , Makarantar na fama da matsalar rashin Silin da kwanon rufe a wasu daga cikin azuzuwan Makarantar, sannan kuma Ruwa na kwanciya Sosai a Makarantar wanda har hakan ya sa ruwan ke neman cin Makarantar”. Inji Ahmad Aminu

“Muna kira ga mahukunta na karamar hukumar Tarauni da su zo domin duba yanayin da makarantar Maza ta GSS unguwa UKU ta ke ciki, domin magance kalubalai da suke addabar Makarantar”. Inji shi

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Jaridar Kadaura24 ta sake tuntubar wasu Mazauna unguwar don tabbatar da mawuyacin halin da Makarantar take ciki, wani dattijo cikin makwabtan Makarantar ya ce halin da Makarantar take cikin ya wuci hankali , Amma ya ce a haka ɗalibai suke shiga kuma suke daukar darasi a Makarantar .

” Wallahi yanzu haka a Makarantar akwai wani ginin bene da daf yake da rushewa Amma a haka ɗalibai suke Hawa shi shiga azuzuwan domin daukar darasi, wanda hakan babbar barazana ce ga rayuwar Malamai da daliban Makarantar”.

Ya ce Makarantar ta zama tamkar hanya domin kowa ta nan yake wucewa, saboda Makarantar ba Kofa kuma wasu daga cikin katangunta sun rushe hakan ta sa kowa ya ke shiga lokacin da ya zo kuma ya fita lokacin da ya so.

IMG 20250415 WA0003
Talla

“Mun yi iya bakin kokarinmu mun kuma sanar da mahukuntan karamar hukumar Tarauni don su kawo ɗauki , Amma har yanzu shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu”. A cewar sa

Don jin shin shugaban karamar hukumar Tarauni Alhaji Ahmad Ibrahim Sekure ya San da matsalar da Makarantar GGSS unguwa uku ta ke ciki?, Kadaura24 ta tuntube shi kuma ya tabbatar mana cewa yasan da matsalolin da ake fuskatan a Makarantar kuma suna yin duk mai yiwa don magance matsalolin.

Da yake magana a madadin Shugaba karamar hukumar jami’in yada labarai yankin Adamu Iliyasu Hotoro ya duk da yake Makarantar tana karkashin kulawar hukumar Kula da Makarantu Sakandire ta jihar Kano , Amma shugaban karamar hukumar ya yi alkawarin gyara Makarantar .

” Tuni Shugaban ya turawa ma’aikatar kananan hukumomin domin ta sahalle masa ya hada hannu da hukumar kula da Makarantun Sakandire don gyara dukkanin Makarantar ta yadda za ta Zama cikin Makarantun da za a rika tunkaho da su a karamar hukumar Tarauni .

Ya yi fatan al’ummar yankin za su Dan jira domin Nan ba da jimawa ba za Fara aikin gyaran Makarantar domin inganta harkokin Ilimi a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...