Bai Kamata Gwamnatin Kano ta yi Auren Zawarawa a Wannan Lokacin ba – Shitu Sani Marshall

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Wani dan kishin jihar kano mai suna Alhaji Shitu Sani Marshall ya ƙalubalanci shirin gwamnatin jihar kano na aurar da zawarawa akan kudin Naira Miliyan 800.

 

” A halin da ake ciki al’umma sun fi bukatar ayi amfani da kudin da za’a kashe a auren zawarawa, wajen baiwa masu kananan masana’antu domin su inganta sana’arsu don bunkasa tattalin arzikin jihar kano da Nigeria baki daya, da Kuma samar da aikin yi ga matasa”.

Talla

Shitu Sani Marshall ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a Kano.

” Ba yin auren ne matsalar ba , a’a yadda magidancin zai kula da gidan sa , idan akai la’akari da yadda ake Kara samun mutuwar aure saboda gazawar mazan wajen daukar nauyin matan da suka aura kamar yadda addinin musulunci ya yi umarni”. Inji Shitu Sani Marshall

Shari’

 

ar zaɓen gwamna: Kwankwaso, Gwamnan Kano, da Wasu Sunyi Addu’a ta Musamman Domin Neman Nasara

Yace Maimakon yin auren na zawarawa kamata yayi gwamnatin ta baiwa wadanda zata yiwa auren jari domin su dogarta da kawunansu daga bisani kuma sai su auren , ta yadda mijin zai iya daukar dawainiyar matarsa da ya’yan da zasu aura.

” A wannan lokaci da tattalin arzikin Nigeria ya shiga wani mawuyacin halin, da za’a Saka kudin da gwamnatin ta ce zata aurar da zawarawa da su har kimanin Naira Miliyan 800, a harkokin kasuwanci babu Shakka kafin shekara da an sami ingantacceen tattalin arziki a jihar kano”. A cewar Shitu Marshall

” A wannan mawuyacin halin wadanda sukai auren da kansu ma suna fuskanta ƙalubale ballantana ka yiwa wadanda basu da aikin yi ko wata tsayayyiyar sana’ar yi, gashi muna gani aure sai mutuwa yake yi saboda matsala tattalin arzikin Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...