Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Date:

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa marigayin ya bar musu wasiyar cewa duk lokacin da ya rasu a binne gawarsa a birnin Madina.

Daya daga cikin iyalansa kuma yar uwa ga uwar gidan marigayin da ta rasu shekaru biyu da suka gabata Hajiya Amina Umar Fulani ce ta shaida hakan a zantawarta da majiyar Kadaura24 ta TST Hausa a safiyar yau Asabar.

InShot 20250309 102512486
Talla

Tace marigayin ya bada wannan wasiyar ne tun bayan rasuwar matarsa marigayiya Hajiya Rabi Tajo Dantata a Madina.

Tun safiyar yau Asabar Shugaban majalisar Malamai ta Kano Shiek Ibrahim Khalil ya sanar da cewa za’ayi sallar Ga’ib ga mamacin Alhaji Aminu Dantata a masallacin Juma’a na Aliyu Bn Abi Dalib dake Dangi a birnin Kano da karfe 2 na rana.

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Ya rasu a Dubai daga nan za’a dauki gawarsa zuwa birnin Madina domin binne gawarsa a kusa da uwar gidansa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...