Zan Sauke duk Ministan da ya gaza sauke nauyin da aka dora masa – Tinubu

Date:

Daga Hafsat Yusuf Sulaiman

 

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya ce shugaba Bola Tinubu ya shafe watanni tun bayan nasarar da ya samu a zaben ƙasar domin ya fitar da manyan manufofin kowane fanni na ƙasar kuma ba zai amince da gazawa daga kowane ne a cikin ministocinsa ba.

 

Ngelale, babban mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin.

Talla

Ya kuma jaddada cewa shugaba Tinubu ya kafa wasu ma’auni na musamman na aiki.

Bai Kamata Gwamnatin Kano ta yi Auren Zawarawa a Wannan Lokacin ba – Shitu Sani Marshall

Ya ce “Tambayar a yanzu ita ce ta aiwatar da doka kuma shugaban kasa ya nuna kamar yadda ya yi a lokacin da yake gwamna a jihar Legas, cewa shi ba wanda ke tsoron korar kowa ba ne.”

“Shi ba wanda ke tsoron sanya takunkumi cikin gaggawa don tabbatar da cewa an samu sakamakon da yake so ba ne.”

Ngelale ya yi karin haske da cewa idan har gwamnatin za ta fuskanci gazawa, laifin ba zai hau kan ministoci kadai ba, maimakon haka, za a dangana ta ne ga shugaban kasa Bola Tinubu.

Ngelale ya kuma bayyana cewa daga lokacin da aka zabe shi zuwa lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, shugaban ya yi amfani da lokacin wajen kafa “jerin kwamitocin kawo sauyi a dukkan bangarori.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...