Daga Halima Musa Sabaru
Makarantar Tuki ta Dangote Articulated Truck, a karshen mako, ta yaye direbobin manyan motoci na musamman guda 50.
Goma daga cikin direbobin mata ne kuma an horar da su kan tukin kariya na tsawon watanni uku, in ji wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina.
Da yake jawabi a wajen bikin yaye daliban, babban darakta na kamfanin simintin Dangote, bangaren sufuri, Obajana Plant, jihar Kogi, Mista Ajay Singh, ya ce makarantar da ake kira Articulated Driving School, na da nufin dakile hadurran mota a Najeriya.

Ya ce, kamfanin yana iya bakin kokarin da wajen magance faruwar haddura, sakamakon tsare-tsare daban-daban su ke da su, tare da hadin gwiwar hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC).
Shugaban sashen kula da harkokin jama’a na kamfanin, Mista Azeez Adeniyi, ya ce makarantar Dangote Articulated Truck Driving School, ba kamarta ba a Nigeria, kasancewar irinta ta farko a tarihin Najeriya.
Ɗan majalisar tarayya na Wudil da Garko ya ƙaddamar da bada tallafi ga kimanin mutane ɗari Uku
Ya kuma bukaci daliban da aka yaye da su yi amfani da horon da suka samu ta hanyar data dace, Inda yace shiga makarantar wata dama ce da ba kasafai ake samun ta ba .
Manajan makarantar, Mista Daniel Marcus Akuso, ya ce kwasa-kwasan da aka koyawa yan rukunin farko sun hada da: Ilimin Civic, Turanci, Lissafi, Tsaro, Gudanar da Motoci, Fasahar kula da motoci , Tsarin Gudanar da DCT, Nazarin Tushen, Lafiya da Kimiyya. Alamomin Hanya da Lambobi.
Sojojin Nijar sun yanke Wutar Lantarki da Ruwa ga Ofishin Jakadancin Faransa
Mista Akuso ya ce a yanzu daliban da suka yaye za su yi aikin na tsawon watanni shida domin su samu kwarewa a aikace.
Da yake jawabi, mataimakin kwamandan tituna, (OC Instructor) na hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC mai kula da makarantar tuki ta Dangote, Engr Mukhtar Umar ya ce hukumarsu na taka rawar gani wajen horas da tsofaffin direbobi da sabbin wadanda aka horas da su.
“Muna koya musu tukin kariya, alamomin hanya, nauyin direba, al’adar tuki, sannan mu ba su shaida zama direbobi ne na musamman.” Inji Engr Umar.
Wakilin Fantique Driving Centre da ke kasar Afirka ta Kudu, Mista Jacques Van Heerden, ya ce wadanda suka kammala karatun sun samu horo kan tukin mota, yana mai tabbatar da cewa idan suka yi aiki da darussan da suka koya daga kwasa-kwasan, hakan zai taimaka wa Najeriya wajen rage hadarin mota.