Sojojin Nijar sun yanke Wutar Lantarki da Ruwa ga Ofishin Jakadancin Faransa

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Shugabannin mulkin soji na kasar Nijar sun yanke wutar lantarki da ruwan sha a ofishin jakadancin kasar Faransa da ke Yamai babban birnin kasar, tare da hana kai musu kayan abinci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na anadole ya rawaito.

 

Rahotanni sun ce gwamnatin mulkin soji ta kuma dauki irin wannan mataki a karamin ofishin jakadancin Faransa da ke Zinder, Tera, Oualam, Ayorou, Dosso, Yamai, Filingue da sauran wurare.

Talla

Shugaban kwamitin tallafawa na kasa na CNSP Elh Issa Hassoumi Boureima ya bukaci dukkan abokan huldar ofisoshin Faransa da ke Nijar da su dakatar da duk wani aikin samar musu da mai, ruwa, wutar lantarki da kayayyakin abinci.

 

“Muna rokon Nigelec da SPEN (SEEN)) da su katse ruwa da wutar lantarki a ofishin jakadancin Faransa, a cikin karamin ofishin jakadancin Faransa na Zinder da Yamai,” in ji shi.

Ɗan majalisar tarayya na Wudil da Garko ya ƙaddamar da bada tallafi ga kimanin mutane ɗari Uku

Bugu da kari, duk abokan huldar da suka ci gaba da taimakawa Faransawa wajen samar da kayayyaki da ayyuka, za a dauke su a matsayin makiyan al’umma Nijar.

Nijar ta fada cikin rudani ne a ranar 26 ga watan Yuli bayan Janar Abdourahamane Tchiani wanda tsohon kwamandan tsaron fadar shugaban kasar ne ya jagoranci juyin mulkin sojoji da suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...