Hajjin bana: Alhazan Najeriya 13 ne suka rasu a kasar Saudiyya

Date:

Daga Hafsat Lawan Sheka

 

Hukumar kula da aikin hajji ta Nigeria NAHCON, ta bayyana cewa Alhazan Najeriya da suka mutu a aikin hajjin bana sun kai 13, kuma wasu 41,632 suka kamu da rashin lafiya a kasar Saudiyya.

 

Shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da alhazan ƙasar, Dr Usman Galadima ne ya bayyana hakan a daren Lahadi a birnin Makkah yayin taron bibiyar yadda al’amura ke tafiya bayan Arafat.

Talla

A jawabinsa, Dr Galadima ya bayyana cewa, jimillar mahajjata bakwai ne suka rasu kafin Misha’ir – tafiya daga Mina zuwa Arafat, da komawa Mina – yayin da wasu shida kuma suka rasu a lokacin Misha’ir.

Sallah: Gwamnan Kano ya nemi afuwar Sarkin Gaya kan abun da ya faru a gidan gwamnati yau

Ya ba da shawarar a riƙa yi wa maniyyata cikakken gwajin lafiya kafin tafiya aikin Hajji tare da ba da takardar shaidar cewa suna cikin ƙoshin lafiya.

NAHCON ta ayyana ranar da za’a fara dawo da Alhazan Nigeria gida

Ya ce kamata ya yi a hana tsofaffin alhazai da majinyata marasa lafiya daga zuwa Jamarat (wurin da alhazai ke jifan shaidan).

Ya kuma buƙaci a riƙa aiwatar da hada-hadar mahajjata kamar yadda hukumomin Saudiyya suka ba da shawara.

Jaridar Daily trust ta rawaito a buƙaci jihohin da ke da motocin ɗaukar marasa lafiya su gabatar da su don aiki tare da jami’an likitocin kula da mahajjata na ƙasa don samun ƙarin haɗin kai a kan lamuran da ke buƙatar gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...