Ayyukan ta’addanci: akwai yiwuwar samun Karancin abinchi a Arewacin Nigeria – Bafarawa

Date:

Rikicin ƙarancin abinci na shirin kunno kai a Arewa sakamakon ayyukan ƴan bindiga – Bafaraw

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya nuna damuwarsa kan ayyukan ƴan bindiga a yankin Arewa-maso-Yamma da kuma Arewa-maso-Gabas, inda ya bayyana fargabar cewa hakan ka iya haifar da matsalar karancin abinci.

 

Bafarawa ya kuma yi gargadin cewa idan ba a dauki tsauraran matakai na dakile tashe-tashen hankula ba, Arewa za ta fuskanci koma bayan ilimi mai tsanani.

Talla

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar PUNCH a jiya Lahadi.

Sallah: Gwamnan Kano ya nemi afuwar Sarkin Gaya kan abun da ya faru a gidan gwamnati yau

A cewarsa, ya kamata sabuwar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dauki batun samar da abinci a matsayin daya daga cikin abubuwan da ta sa gaba.

 

Bafarawa ya ce, “Maimakon maganar naɗin ministoci, tallafin mai da kuma tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da batun samar da abinci domin a halin da muke ciki, nan da watanni uku masu zuwa, tabbas za mu fuskanci matsaloli a Najeriya, musamman a Arewa-maso-Yamma.

NAHCON ta ayyana ranar da za’a fara dawo da Alhazan Nigeria gida

“’Ƴan bindiga sun ki barin manoma su yi noma. Wannan lamari dai ya na da matukar hadari, ba wai kawai yan bindigar na kashe mutane ba, har ma da karancin abinci zai yi tsanani nan da wasu watanni masu zuwa, musamman a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Don haka mu na son gwamnati ta farka ta yi wani abu a kai,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...