Daga Kamal Yakubu Ali
Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya bukaci gwamnatoci a matakai daban-daban na kasar nan da su maida hankali wajen gudanar da ayyukan da zasu rage talauci a tsakanin al’umma.
Dan kasuwar ya shawarci gwamnoni a wadannan shekaru biyu da suka rage masu duba da irin manyan ayyuka da suka gudanar a shekaru biyun da suka gabata, a yanzu lokaci ne da ya kamata da su karkata wajan aiwatar da kananan ayyuka da za su taba rayuwar al’umma kai tsaye, wanda hakan zai rage aikata kanana laifuka a tsakanin allumma.
Yakasai ya bayyana hakanne a yayin bikin rufe karatun littafin Ashfa wanda Malam Abdulkadir Shehu mai Anwar ya gabatar a unguwar Tudun Yola dake karamar hukumar Gwale.

“A halin yanzu mutane suna cikin halin matsi da talauci wanda yake hana su walwala, a don haka ya kamata gwamnati ta yi tunanin samar da ayyukan da za su taba rayuwar al’umma kai tsaye wanda zai rage musu radadin halin da suke ciki”. Inji SKY
Sky ya bukaci gwamnoninmu da su ware wasu makudan kudade da za su rinka tallafawa yan kasuwa da sauran masu gudanar da sana’o’i daban-daban, domin karfafa musu gwaiwa wajan bunkasa kasuwancinsu.
Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki
Ya ce a wannan lokaci da yawa daga cikin ‘yan kasuwa masu karamin karfi jarinsu ya karye, ya kamata gwamnatin Tarayya da gwamnoni jihohi musamman na Arewacin Nigeriya su fito da wasu hanyoyi da zasu tallafawa al’ummarsu yadda za a rage talauci da fatara da samar da ingantacciyar Rayuwa da zaman lafiya a cikin al’umma.
Sky ya shawarci gwamnatin jihohi dasu samarwa da mañoma Taki kyauta domin a halin yanzu manoma suna bukatar tallafi daga gwamnati domin basa iya sayan Taki sakamakon tsadar da yayi , wanda hakan ne zai taimaka wajan kokarin da gwamnati take na samarda abinci a cikin farashi mai sauki .
Ya kuma bukacesu dasu samarda Gidaje kanana a gurare daban daban, duba da cikonso da ake fama dashi acikin gari wanda yana taimakawa wajan haifarda aikata kananan laifuka a a tsakanin matasa .kuma idan akayi hakan ma aikata da sauran masu karamin karfi zasu amfana da wannan aiki.
Taron ya samu halartar alumma da dama da suka hadarda limamai da suka hadarda hakimin kauran Namoda a jihar Zamfara da sauransu.