Kwamishinan Sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, ya janye matsayin da ya dauka na tsayawa beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a gaban kotu.
Sanarwar hakan na kunshe ne a wata takarda da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Abdullatif Auta, ya fitar a ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, Kwamishina Namadi ya rubuta wa kotu wasika ya na bayyana aniyarsa ta janye belin da ya tsaya wa Sulaiman Aminu Danwawu, wanda Hukumar NDLEA ke tuhuma da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Dalilina na karbar belin Danwawu – Kwamishina Namadi
Kwamishinan ya ce ya dauki matakin janye belin ne saboda dalilai na kashin kai da kuma bukatar kare mutuncinsa da martabar ofishin da yake rike da shi.
Ya ce lokacin da ya tsaya wa Danwawu beli, ya yi hakan ne saboda alakar jini da ke tsakaninsu da kuma jin kai, amma ba saboda yana goyon bayan ayyukan da ake tuhumarsa da shi ba.