Sallah: Gwamnan Kano ya nemi afuwar Sarkin Gaya kan abun da ya faru a gidan gwamnati yau

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa

 

Gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya nemi afuwar mai martaba sarkin Gaya sakamakon saboda yadda ya kirawa shi da sunan Mai martaba Sarkin Rano yayin da ya je gidan gwamnati don yiwa gwamnan Barka da Sallah.

 

” Ina Jan hankalin yan Protocol din gwamna, ya kamata su sani duk wanda aka baiwa Protocol din gwamna ba abu ne mai sauƙi ba, domin Protocol kai ne mai mu’amala da manyan mutane da jagorori da dukkan baki da zusu zo wajen gwamna, don haka bai kamata ku rika wasarairai da aikin ku ba”.

Da dumi-dumi: Muhuyi ya kwato motocin kwashe shara 13 da suka bata a gwamnatin data gabata

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin mai martaba sarkin Karaye, wanda ya je domin yiwa gwamnan Barka da Sallah a gidan gwamnatin kano.

Tallah

” Yau da safe na karɓi bakuncin mai martaba sarkin Gaya lokacin da na tashi zan yi magana Protocol sun miko min sunan Sarkin Rano da sunan cewa shi ne sunan Sarkin Gaya, Kuma na ambaci sunan Sarkin Rano a maimakon Sarkin Gaya Kuma a gaban Sarki Gaya”. Inji Abba Gida-gida

Abba Kabir Yusuf ya ce bai ji dadin abun da ya faru ba, Kuma ya nuna matukar bacin ransa kan wannan Abu da ya faru, sannan ya ja hankalinsu da su guji sake yi masa haka a nan Gaba.

Talla

” Ina amfani da wannan dama in baiwa mai martaba sarkin Gaya hakuri bisa wannan kuskure da akai, da fatan Allah ya sa a gyara a nan Gaba”. A cewar Abba Gida-gida

Kadaura24 ta rawaito cewa Protocol dai wani sashi ne a gidan gwamnati da suke kula da baki da tsare-tsaren gwamna a kowanne lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...