Tsananin zafi ya kwantar da mahajjata 6,700 a Saudiyya

Date:

Cibiyoyin dake kula da waɗanda zafin rana ya illata a wuraren ibada masu tsarki na ƙasar Saudiyya na ci gaba da samun hauhawar mutanen da ake kwantarwa saboda jigata.

Ana alaƙanta lamarin da gazawar mahajjata wajen bin ƙa’idojin kare kai daga tsananin zafin rana da ake a kasar Saudiyya.

Tallah

Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya ta faɗakar da mahajjata game da hatsarin tsananin zafin rana, inda ta buƙace su da su riƙa sanya ɓaƙin tabarau da kuma shan ruwa sosai, sannan su guje wa zirga-zirgar da ba ta wajaba ba.

Ganduje ya Magantu kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da gwamnatin Kano ta yi

Haka nan ma’aikatar ta buƙaci maniyyatan da su guje wa tsayuwa na tsawon lokaci.

BBC Hausa ta rawaito Ma’aikatar ta ce a halin yanzu waɗanda tsananin zafin ranar ya kwantar sun kai 6,700 tun bayan fara aikin hajjin bana.

A jiya an samu irin wannan matsala mafi yawa, inda zafin ya illata mutum 2,200, cikinsu har da mutum 261 waɗanda suka shiga mummunan yanayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...