Daga Rahama Umar Kwaru
Ζungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta ce akwai yiwuwar nan da lokaci kaΙan farashin man fetur zai zarce naira 600 a kan kowace lita.
IPMAN ta ce hakan zai faru ne sanadiyyar rashin tabbas kan samuwar dala ga Ζ΄an kasuwa masu shigo da tataccen man fetur daga Ζasashen waje.
Ganduje ya Magantu kan dakatar da albashin ma’aikata dubu 10 da gwamnatin Kano ta yi
Bayanai sun nuna cewa da zarar ‘yan kasuwa masu zaman kansu suka fara shigo da man fetur a wata mai kamawa, farashin litar mai zai haura sama a faΙin Ζasar.

A lokacin da yake tabbatar wa BBC da wannan batu, shugaban Ζungiyar dillalan man fetur Ιin a yankin Arewacin Najeriya, Bashir Dan-Mallam ya ce dole ne sai gwamnati ta Ιauki matakan da suka dace domin hana faruwar hakan.
Dan-Mallam ya ce samuwar dalar a wadace ga Ζ΄an kasuwa za ta hana hauhawar farashin na litar mai.
A yanzu dai kamfanin man fetur na Ζasar NNPC ya ce zai riΖa shiga da kashi 30% na man fetur Ιin da Ζasar ke buΖata, yayin da Ζ΄an kasuwa za su shigar da sauran.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, wani lamari da ya haifar da tashin farashin litar man fetur a faΙin Ζasar.